An sa dokar ta-baci a Diffa
February 11, 2015Talla
Matakin dai ya zo bisa yadda tsagerun Boko Haram suka zafafa kai farmaki 'yan kwanakinnan. Sanarwar kafa dokar ta-bacin ta biyo bayan da ministan tsaron Jamhuriyar Nijar, ya yi gargadi kan halin da yankin Diffa ya shiga, inda jama'a ke ci gaba da tserewa don gudun kara dagulewar tashen hankali a yankin. Kungiyar Boko Haram dai ta zafafa farmaki a yankin cikin makwan jiya, inda na baya-baya shine harin kunar bakin wake da wata mace ta kai shekaran jiya Litinin, abin da ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane shida, yayinda wasu da dama suka jikkata. A ranar Lahdi da ta gabata ne, Najeriya da makobtanta suka amince da hada wata rundunar sojoji da za ta baiwa Boko Haram kashi.