An sace ma'aikatan MDD a Sudan
January 29, 2015Talla
An kama ma'aikatan na Majalisar Dinkin Duniya 'yan kasar Bulgeriya shida, a kasar ta Sudan yayin da suke kan aiki. Mutanen da ake aikin samar da abinci, an tilastawa jirginsu mai saukar angulu sauka, a yankin da gwamnati da 'yan tawaye ke fada da juna. An dai yi imanin cewa 'yan tawayen SPLM su ne suke rike da ma'aikatan na Majalisar Dinkin Duniya.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Umaru Aliyu