An sake artabu a zirin Gaza
November 13, 2018Rahotannin da ke fitowa daga yankin zirin Gaza, na cewa wasu Falasdinawa masu gwagwarmaya da makamai sun kai hare-haren rokoki kan Isra'ila, a wani artabun da ake bayyana shi da cewar ba a ga irinsa ba tun gumurzun shekara ta 2014.
Bayanai sun ce Isra'ilawan a nasu bangaren, sun kai wasu munanan hare-haren da jiragen yaki ta sama inda bangaren falasdinawa ya ce mutum shida sun halaka, ciki kuwa har da 'yan tawaye biyu.
Jami'ai a Gazar sun kuma ce jiragen na Isra'ila sun ragargaza gidan talabijin na Hamas, yayin da a bangaren Isra'ila aka sami akalla mutum 20 da suka jikkata ciki har da wata dattijuwa 'yar shekaru 60 da haihuwa.
Da jijjifin safiyar Talatar nan ma dai jami'an Isra'ila sun ce sun tsiontsi gawar wani, karkashin baragunan gine-gine a kudancin birnin Ashkelon, wanda suka yi amannar rokokin na bangaren falasdinun ne suka yi sanadinsa.