An sako fursunonin siyasa 80 a Sudan
February 19, 2018Talla
A farkon shekarar 2018 jami'an tsaro suka kame mutane da dama ciki har da jagororin jam'iyyun adawa, yayin wata arangama da ta barke tsakanin 'yan sanda da fararen hula a lokacin gudanar da zanga-zangar nuna adawa da matsin tattalin arziki da hauhawar farashin kayan abinci.
Amma har yanzu ana ci gaba da tsare wasu jiga-jigan 'yan adawa, abin da ya sa jama'a suka yi ta rera wakokin 'yanci da taken kasar a gaban gidan yarin da nufin nuna matsin lamba ga gwamnati domin sako sauran mutanen da ake tsare da su.
A bara kasar Amirka ta janye wa Sudan takunkumin sama da shekaru 20, inda ta bukaci hukumar ba da lamuni ta duniya da ta yi wa Sudan sassauci a wani mataki na farfado da tattalin arzikinta.