An sako ma'aikatan MDD da aka kama a Sudan ta Kudu
November 2, 2015Talla
Majalisar Dinkin Duniya ce ta sanar da hakan a wannan Litinin inda ta ce ko baya ga mutanen ta yi nasarar karbo kwale-kwale ukku da wani tanki mai dauke da lita dubu 55 na man fetur da ma wasu na'urorin sadarwa da kuma bindigogi bakwai daga cikin 16 na sojojin rundunarta wadanda 'yan tawayen Sudan ta Kudu din suka kame tare da mutanen.
Ranar 26 ga watan Oktoban da ya gabata ne 'yan tawayen na Sudan ta Kudu suka kame ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya 31 da suka hada da sojojin rundunar zaman lafiya ta Majalisar a wannan kasa wato Muniss a saman wani kogi kafin daga bisani su sako sojojin amma sun ci gaba da rike sauran ma'aikatan da kayan aikinsu.