An sallami babban hafsan sojan Sudan ta kudu
April 24, 2014Talla
Shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir ya sallami babban hafsan sojojin kasar, bayan da rahotanni suka tabbatar da cewa 'yan tawaye sun samu nasarar kwace rijiyoyin mai da ke arewacin kasar. Ba a dai bada dalilin koran janar James Hoth Mai, sai dai kawai gidan talabijin na gwamnati ya sanar da cewa an maye gurbinsa da Janar Paul Malong. To amma ana kyautata zaton ran shugaban kasa ya baci, bisa koma bayan da rundunar sojan kasar ke samu, a yakinsu da 'yan tawaye masu goyon bayan Riek Macher, wanda har ta kai yanzu aka fatattakin sojan gwamnati daga rijiyoyin man kasar mafiya girma.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mohammed Nasir Awal