An sallami Nelson Mandela daga asibiti
December 27, 2012Talla
Nelson Mandela dai ya yi fama ne da cutar huhu gami kuma da tiyata da aka yi masa ta cire duwatsun matsarmama.
Mahukuntan Afrika ta Kudun sun ce jami'an kiwon lafiya za su cigaba da kula da lafiyar Mr. Mandela dan shekaru casa'in da hudu a gidansa da ke birnin Johanesburg har ya samu ya murmure sosai.
Nelson Mandela dai wanda ke zaman shugaban Afrika ta Kudu bakar fata na farko ya shafe kimanin shekaru biyu baya fita bainar jama'a ko kuma hallartar duk wasu taruka da ake shirya a kasar.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Halima Balaraba Abbas