An samar da majalisar ministoci a Sudan
September 6, 2019Talla
A wani jawabi da ya yi gaban 'yan jarida a Khartoum babban birnin kasar, Abdalla Hamdok, ya ce burinsu yanzu shi ne kawo karshen yaki a Sudan tare da samun zaman lafiya.
Kafa gwamnatin dai na daga cikin yarjeniyar gwamnatin hadaka ce da aka cimma a tsakanin wakilan fararen hula da soji na tsawon shekaru uku.
Mata hudu ne daga cikin minsitoci 18 da aka sanar a ranar Alhamis, ciki har da mace ta farko da aka bai wa ministar harkokin kasashen ketare, Asma Mohamed Abdallah.
Haka nan Firai Ministan ya bayyana tsohon jami'in bankin duniyan nan Ibrahim Elbadawi, a matsayin ministan kudin kasar.