An sami ci gaba a fannin kiwon lafiyar yara
September 13, 2013Talla
Lisafin dai ya yi daidai da rabi na yawan yaran da ke mutuwa a duniya tun daga shekarun 1990. Duk da ma cewar a kowace rana yara 'yan ƙasa da shekaru biyar dubu 18 ke mutuwa.
A cikin wani rahoto na haɗin gwiwa da ƙungiyar lafiya ta duniya WHO ko kuma OMS da UNICEF da kuma bankin duniya suka wallafa a yau, sun ce ana kan hanyar rage mace-macen yara da kishi biyu bisa uku kafin nan da shekarun 2015.
Rahoton ya ce yawancin mace-mace na yara na faruwa ne a cikin ƙasashen Kwango da Pakistan da China da Indiya da kuma Najeriya ƙasashe biyu na ƙarshe inda lamarin ya fi yin ƙamari.
Yawanci ana samu mutuwar yara ne wajen haifuwa da sauran cututtuka irinsu gudawa.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman