Coronavirus ta bulla a Saudiyya
March 2, 2020Talla
Hukumomin kasar Saudiyya sun tabbatar da samun mutum na farko da ya kamu da cutar Coronavirus, hukumomin kiwon lafiya sun ce mutumin dan salin kasar ne da ya dawo daga kasar Iran.
Yanzu haka dai akwai mutane 1,700 da suka kamu da cutar Coronavirus a kasashen da ke yankin Gabas ta Tsakiya kadai.