Nana Akufo-Addo ya samu wa'adi na biyu na mulki
December 9, 2020Hukumar zabe a Ghana ta gaza bayyana sakamakon zaben shugaban kasar da na 'yan majalisun dokoki a cikin wa'adin da aka kayade na sa'oi 48. A jiya cikin dare alkali kana shugabar hukumar zaben EC Jean Mensah, ta kira wani taron manema labarai inda ta nuna cewar kawo yanzu sakamako zabukan daga jihohi 14 cikin 16 take dauke da su. Wadanda a ciki a kan iya tantance kaso 78% cikin dari wanda ga alkalluman da majiyoyi suka bayyana da kuri'u kalilan ne shugaban kasa mai ci ya yi wa abokin takarar sa tshohon shugaba John Mahama tazara. To sai dai kuma wasu sabbin bayyanai da suka zo sun nuna cewar a sakamakon yankuna 7 daga cikin 16 da ake da su da hukumar ta fitar, ya nuna madugun adawa John Dramani Mahama a matsayin wanda ke kan gaba ga abokin fafatawarsa kuma shugaba na yanzu Nana Akufo-Addo. A halin da ake ciki Akalla mutane biyar ne suka hallaka wasu 17 kuma suka jikata a tashe-tashen hankulan da aka samu a yankunan Ghana da dama a yayin manyan zabukan kasar na ranar Litinin.