An sassauta dokar ta-bace a jihar Diffa
October 31, 2018Matakin sassaucin ya tanadi bai wa jama'a damar gudanar da harakokinsu daga karfe biyar na safe zuwa karfe sha daya na dare.
Al'ummar jihar ta Diffa wacce ta jima tana korafi da wannan doka da ta ce ta kawo cikas ga rayuwar jama'a da harakokinsu na yau da kullum ta yaba da matakin sassauta dokar. Masu shaguna da tebura da masu sana'ar acaba da dai sauran harakokin kasuwanci sun bayyana jin dadinsu da yadda aka kara tsawaita wa'adin soma aikin dokar da dare inda a yanzu suke da damar ci gaba da harakokinsu kasuwancinsu har zuwa bakin magariba.
Sai dai duk da haka wasu al'ummomin jihar ta Diffa sun bayyana bukatar kara yin sassauci ga dokar musamman dangane da abin da ya shafi amfani da ababen hawa a cikin dare ta yadda wadanda suka samu wata larura ko ta rashin lafiya ko kuma haihuwa a tsakiyar dare su iya amfani da mota domin zuwa assibiti.