1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An shiga zagaye na karshe na taron tantance makomar lardin Kosovo

March 10, 2007
https://p.dw.com/p/BuQ1

Manyan shugabannin Sabiya da na Albaniyawan Kosovo sun shiga zagaye na karshe na wata tattaunawar da suke yi a Vienna babban birnin Austria, akan wani shirin MDD da zai tantance makomar lardin Kosovo. Shugabannin kabilar Albaniyawan Kosovo sun albarkaci wannan shiri amma jami´an Sabiya sun yi watsi da shi suna masu korafin cewa ya tanadi bawa lardin na Kosovo ´yancin kai sannu a hankali. A bara aka fara shawarwarin akan makomar Kosovo amma gaba daya suka cije kuma ba´a tsammanin samun wani ci-gaba a taron na yau asabar. Shugaban Albaniyawan Kosovo Hashim Thaqi ya nuni da cewa.

“Mu dukkan mu a Kosovo muna aiki tukuru don yanke wata shawara mafi dacewa, shawara ta samun ´yanci. Masalaha a garemu, mu ´yan Kosovo ita ce girmama bukatar al´umar mu. Wato Kosovo ta zama kasa mai cikakken ´yanci.”

Bayan taron za´a mikawa kwamitin sulhu, shawarar da MDD ta bayar game da makomar lardin na Kosovo don ya albarkace shi.