1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An soki hukuncin da aka yanke wa masu fafatuka a Angola

Mohammad Nasiru AwalMarch 30, 2016

Masu shari'a a Angola sun yi tir da hukuncin da ake yanke wa 'yan fafatuka 17 bisa zargin yunkurin kifar da gwamnati.

https://p.dw.com/p/1IMEI
Angola Justiz Symbolbild
Hoto: DW/N. Sul de Angola

Ma'aikatan shari'a a kasar Angola sun yi tir da hukuncin da ake yanke wa wasu 'yan fafatuka 17 na wata kungiya da ake kira Luanda Book Club. Daukacin masu shari'a a kasar ta Angola sun yi amanna cewa ba a yi wa mutanen adalci ba, suna masu cewa hukuncin na da alaka da wani mulki na kama karya, kuma zai yi mummunan tabo ga tsarin shari'ar kasar. Francisco Viena mai shari'a ne a kasar ta Angola.

"A gani na wannan shari'a ba ta da wani hurumi a shari'ance. Ba a yi adalci ba. Kotuna ba za su iya yanke hukuncin da zai tauye 'yancin walwala ba. Wata kotu ta wata kasar mulkin kama karya ta yanke hukuncin."

A ranar Talata wata kotu a Angola ta yanke wa masu fafatukan 17 hukuncin daurin shekaru biyu zuwa takwas a gidan maza bayan ta same su da laifin kulla wata makarkashiyar hambarar da gwamnatin Angola. Tuni dai lauyoyinsu suka ce za su daukaka kara a kotun kolin kasar.