An soki shirye-shiryen Isra'ila na gina sabbin matsugunan Yahudawa
September 28, 2011Gamaiyar ƙasa da ƙasa ta yi suka da kakkausan lafazi game da shirin Isra'ila na gina sabbin gidaje dubu da 100 a yankin Larabawa na gabacin birnin Ƙudus. Shugaban tawagar tattaunawa na Falasɗinu Saeb Erekat ya ce wannan matraki wani kunen uwar shegu ne ga ƙoƙarin ƙasashen duniya na wanzar da zaman lafiya.
"Sau dubu da 100 Isra'ila ta yi fatali da fara tattaunawa game da samar da ƙasashe biyu maƙwabtan juna."
Ita kuwa sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton cewa ta yi matakin zai mayar da hannun agogo baya a ƙoƙarin maido da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasɗinu.
"Matuƙar babu wata tattaunawa kai tsaye to babu abin da zai canza a ƙasa. Idan da tattaunawar to za a warware batun shata kan iyakoki da wurin kowane ɓangare zai yi gini."
A kuma birnin Berlin wani kakakin ma'aikatar harkokin waje, ya ce ministan harkokin wajen Jamus Guido Westerwelle ya nuna damuwa game da matakin gina sabbin matsugunan Yahudawan. Ita kuwa jami'ar kula da harkokin ƙetare na ƙungiyar tarayyar Turai Catherine Ashton kira ta yi ga Isra'ila da ta janye wannan ƙuduri.
Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal
Edita: Yahouza Sadissou Madobi