An soma tattaunawa a babban taron Majalisar Dinkin Duniya
September 24, 2019A cikin jawabin da Shugaban na Amirka ya yi Donald Trump ya ce Amirka ba ta neman yi fada da kowace kasa, abin da suke fata shi ne hulda ta gari da dukkanin kasashe domin samun zaman lafiya. Sai dai ya yi gargadin cewar zai kare manufofin Amirka ta kowane hali. A shekara ta 2017 a lokacin irin wannan taro a karon farko da ya bayyana a zauren MDD Donal Trump ya yi furcin cewar Amirka za ta kawar da Koriya ta Arewa daga doron kasa. Sai dai masu yi nazari a kan al'amura na gani cewar za a iya samun babbar baraka a nan gaba a taron tsakanin shugabannin kasashen duniyar a kan batu kare muhali, wanda daman Donald Trmp din ba yarda da akwai cnjin yanayi ba. Shugaban na Amirka ya dau magana ne bayan da shugaban Kasar Brazil Jair Bolsonaro ya soma yin bayyani da farko wanda ya zargi kasashen duniya a cikin jawabin da ya yi da cewar ana neman a yi wa Brazil din mulkin mallaka hasali ma game da batun dajin Amazon wanda ya ce kasashen duniya na son yin musu katsa landan.