An tabbatar da zaɓen Biden a Amirka
December 15, 2020Talla
Wakilai 306 ne suka zaɓi Mr. Biden, yayin da shugaba mai barin gado Donald Trump wanda har yanzu bai amince da shan kaye ba, ya ke da wakilai 232.
A ranar 6 ga watan Janairu ne dai 'yan majalisar ƙasar za su tabbatar da zaɓin wadannan wakilai, inda mataimakin shugaban ƙasa Mike Pence zai jagoranci zaman.
An dai tsaurara matakan tsaro a wasu jihohin da wakilai masu zaɓen suka hallara domin kaɗa kuri'un tare da bin dokokin kariyar cutar corona.
Zaɓaɓɓen shugaban na Amirka Joe Biden ya bayyana zaɓen nasa a matsayin nasara ga dimukuraɗiyya da ma Amirka baki ɗaya.