An kashe jakadan Chaina a Isra'ila
May 17, 2020Talla
Majiyoyin tsaro a Isra'ila sun ce an taras da gawar jakadin Chaina a Isra'ila a gidansa da ke kusa birnin Tel-Aviv. Du Wei dan shekaru 57 tsohon jakadin Chaina a Ukraine wanda aka nadashi jakadi a cikin watan Maris da ya gabata a Isra'ila, ya mutu a gidansa da ke a Herziliya kusa da Tel-Aviv. Ya zuwa yanzu hukumomin sun ce ba su da masaniya a game da mutuwar jami'in diplomasiyar wanda iyalensa ba tare suke da shi ba a can.