An tsagaita bude wuta a birnin Khartoum
June 10, 2023Talla
Mazauna birnin na Khartoum suka ce ba su ji karar harbe-harbe ba tun lokacin da sabuwar yarjejeniyar da aka rattaba hannu a kanta bisa jagorancin Amurka da Saudiyya ta fara aiki a ranar Asabar.
Al'ummomi sun shaida wa manema labarai cewa sun fara gudanar da al'amuransu na yau da kullum, inda wasu suka je neman kayayyakin masarufi.
Kafafen yada labarai sun jiyo ministan harkokin wajen Saudiyya na cewa bangarorin biyu sun amince da tsagaita bude wutar ne don ba da damar isar da kayan agaji kasar, kana za a ci gaba da tattaunawa don sasanta rikicin da aka yi kusan watanni biyu ana yi.
Sai dai bangarorin biyu da ke neman kakkange madafun iko ya sha alwashin mayar da raddi muddin ya fuskanci wata takalar fada.