An tsagaita wuta a Gaza
August 5, 2014Isra'ila da kungiyar tsagerun Falasdinawa ta Hamas sun fara aiki yarjejeniyar tsagaita wuta ta tsawon sa'o'i 72, kwanaki uku ke nan, wadda ta bayar da damar gudanar da ayyukan jinkai a yankin Zirin Gaza na Falasdinu, wadda aka gabatar a wajen taron neman sulhu na birnin Alkahira na kasar Masar. Yarjejeniyar ta wannan Talata tuni ta fara aiki, kuma duk bangarorin biyu suna girmamawa.
A ranar Litinin Isra'ila ta yi gaban kanta wajen tsagaita wuta na tsawon sa'o'i bakwai, amma daga bisani ta koma gudanar da ayyukan soji a yankin Zirin Gaza. Wannan yarjejeniyar tsagaita wutar tana zuwa bayan rikicin tsakanin bangarorin Isra'ila da Hamas ya yi sanadiyar Hallaka Falasdinwa kusan 2000 da kuma Yahudawa fiye da 60.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Usman Shehu Usman