1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tsige firaministar Senegal daga muƙaminta

July 5, 2014

A wani mataki na mayar da martani kan faɗuwar da ta yi a zaɓen ƙananan hukumomin ƙasar, Shugaba Macky Sall ya cire Aminata Toure daga muƙaminta.

https://p.dw.com/p/1CWDH
Hoto: Reuters

Al'umma a ƙasar Senegal na zaman jiran naɗin sabon Firaministan ƙasar, bayan da Shugaban ƙasar Macky Sall ya tsige Firiministan Aminata Toure a jiya Jumma'a (04.07.2014), sakamakon faɗuwar da ta yi a zaɓen kananan hukumomin da aka gudanar a makon jiya.

Ita dai tsofuwar Firaministar, ta yi takara ce ta neman shugabancin ƙaramar hukumar Grand Yoff, ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin birnin Dakar, inda magajin garin birnin na Dakar mai barin gado Khalifa Sall ya doketa. Ana ganin cewar tsige Firaministan ta Senegal, zai bai wa shugaba Macky Sall wata dama, ta kawo sauye-sauyen da ya yi alƙawarin yi, cikin tafiyar da mulkinsa.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Abdourahamane Hassane