An tsige firaministar Senegal daga muƙaminta
July 5, 2014Talla
Al'umma a ƙasar Senegal na zaman jiran naɗin sabon Firaministan ƙasar, bayan da Shugaban ƙasar Macky Sall ya tsige Firiministan Aminata Toure a jiya Jumma'a (04.07.2014), sakamakon faɗuwar da ta yi a zaɓen kananan hukumomin da aka gudanar a makon jiya.
Ita dai tsofuwar Firaministar, ta yi takara ce ta neman shugabancin ƙaramar hukumar Grand Yoff, ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin birnin Dakar, inda magajin garin birnin na Dakar mai barin gado Khalifa Sall ya doketa. Ana ganin cewar tsige Firaministan ta Senegal, zai bai wa shugaba Macky Sall wata dama, ta kawo sauye-sauyen da ya yi alƙawarin yi, cikin tafiyar da mulkinsa.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Abdourahamane Hassane