An tura karin sojojin Afghanistan zuwa yankin Helmand
December 23, 2015Talla
A wannan Larabar an tura karin dakarun Afghanistan yankin Helmand bayan da Taliban ta kame wasu wurare a yankin da ake noman ganyen opium ciki. Hakan ya sa a karon farko cikin watanni 14 an sake girke dakarun Birtaniya a lardin mai fama da rikici. Mazauna da ke tserewa daga yankin sun ce mayakan Taliban na kashe sojojin da suka kama yayin da 'yan Taliban din ke kara dannawa tsakiyar lardin. Yanzu haka dai ana kara nuna fargabar cewa lamuran tsaro za su tabarbare a yankin. Mukaddashin gwamnan Helmand Mohammad Jan Rasoolyar ya fada wa kamfanin dillancin labarun AFP cewa an gaggauta tura karin dakarun gwamnati don karfafa guiwar 'yan sanda da sojojin da aka yi wa kawanya a tsakiyar lardin.