An yaba da yadda zaben kasar Cote d'Ivoire ya gudana
October 26, 2015Talla
Masu saka ido kan zabe na kasar Cote d'Ivoire sun ce an kwatanta gaskiya da adalci yayin zaben shugaban kasa da ya gudana a wannan Lahadi da ta gabata.
Olusegun Obasanjo da ke zama Shugaban tawogar masu saka ido na kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma kana tsohon shugaban Najeriya, ya ce sakamakon zaben zai tabbatar da abin da mutane suke bukata. Tuni kungiyar Tarayyar Afirka ta amince da wannan matsayi, yayin da 'yan kasar suke jira a bayyana wanda ya lashe zaben.
Shugaba Alassane Ouattara dan shekaru 73 da haihuwa yana fuskanci kalubale daga 'yan takara shida a kasar da ke da mutane kimanin milyan 23. Kasar ta Cote d'Ivoire da ke yankin yammacin Afirka tana cikin kasashe masu samun bunkasa na tattalin arziki.