1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An yake wa dakarun Sudan hukuncin kisa

Mouhamadou Awal Balarabe
December 30, 2019

Kotun ta samu jami'an tsaron Sudan 27 da laifin kashe Ahmed al-Kheir Awadh mai zanga-zangar neman sauyi, lamarin da ya sa ta yanke musu hukuncin kisa ta hanyar ratayewa.

https://p.dw.com/p/3VUiJ
Sudan Soldaten in Khartum
Hoto: Getty Images/AFP/M. El-Shahed

Wata kotu a kasar Sudan ta yanke wa wasu jami'an leken asiri 27 hukuncin kisa bayan da aka same su da laifin azabtarwa da ya kai ga mutuwar wani mai zanga-zangar nemen sauyi a watan Disamban bara. Cikin hukunci da ya yanke, alkali Sadok Abdelrahman ya nemi a rataye wadanda suka yi sanadin mutuwar malamin makaranta Ahmed al-Kheir Awadh bayan kama shi a  jihar Kassala da ke gabashin kasar.

Idan za a iya tunawa a ranar 19 ga Disamban 2018 ne daruruwan ‘yan kasar ta Sudan suka fara zanga-zanga bayan da gwamnati ta ninka farashin biredi a daidai lokacin da ake tsaka da fama da komabayar tattalin arziki. Wannan zanga-zangar ta rikide zuwa boren wanda yayi awon gaba da kujerar mulkjin  Shugaba Omar el-Beshir bayan shekaru 30 na mulki.

A cewar kungiyar Amnesty International, akalla mutane 177 sun mutu a lokacin da sojoji suka yi amfani da karfi wajen murkushe boren a ranar 3 ga watan Yuni a birnin Khartoum.