Saudiyya: Hukunci kisa kan makisan Khashoggi
December 23, 2019A kasar Saudiyya, Kotun birnin Ryad ta yanke hukuncin kisa kan biyar daga cikin mutane 11 da aka gurfanar a gabanta kan kisan Jamal Khashoggi shahararren dan jaridar nan na mujalla Washington Post dan asalin kasar Saudiyya wanda aka halaka a karamanin ofishin jakadancin Saudiyya da ke a birnin Istanbul a watan Oktoban 2018.
Sai dai kuma kotun ta wanke wasu mutane biyu da ake zargin sune a sahun gaban kisan dan jaridan, wato Saoud al-Qahtani mashawarci ga yarima mai jiran gado Mohamed Ben Salman da kuma Janar Assiri mataimakin shugaban hukumar leken asirin kasar a bisa rashin samun kwararan hujjoji na zargin da ake yi masu.
Kotun ta birnin Riyad ta kuma yanke hukuncin daurin shekaru 24 ga wasu mutanen uku, kana ta sallami sauran. Kotun ta ce zaman shari'ar kisan dan jaridan ya gudana ne a gaban wakillan kungiyoyin kasa da kasa da kuma 'yan uwan dan jaridan.
A baya dai hukumar leken asirin Amirka ta CIA da kuma MDD sun zargi yarima Ben Salman da kitsa kisan dan jaridan, zargin da amma yariman ya yi ta musantawa.