Mahara a Zamfara sun yi garkuwa da mutane 20
August 16, 2021Talla
Bayan kisan 'yan bindigar sun kuma yi garkuwa da mutun 20 ciki har da daliban makarantar 15 a cewar Abdullahi Aminu daya daga shuwagabannin makarantar a yayin zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na AFP. Majalisar Dinkin Duniya dai ta ce akalla dalibai 1000 ne aka yi garkuwa da su a sassan jihohin Najeriya dabam-daban tun daga watan Disanban bara zauke yanzu, kana kuma galibin wadanda aka sakin sun kubuta ne bayan an biya kudin fansa, ko da ya ke har yanzu 'yan bindigar da ke addabar yankin na cigaba da garkuwa da wasunsu da dama.