An yi jana'izar Mwai Kibaki a Kenya
April 29, 2022Talla
Gwamnatin Kenya ta gabatar da jana'izar bankwana ga tsohon shugaban kasa Mwai Kibaki, wanda ya mutu a makon jiya yana da shekaru 90.
Marigayi Kibaki da aka yaba da kamun ludayinsa, ya mulki Kenya ne a tsakanin shekarar 2002 zuwa 2013.
Shi ne shugaban da ya karba daga hannun Daniel arap Moi wanda ya mulki Kenyar na tsawon shekaru 20.
An kwantar da gawar marigayin Shugaba Kibaki ne a babban filin wasa na Nyayo da ke Nairobi babban birnin kasar, inda dubban mutane suka yi masa gani na karshe.
Shugabannin kasashen Afirka da dama ne suka halraci jan'aizar ta marigayi Mwai Kibaki.