1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Habasha: Amirka da Kenya sun nemi a tsagaita wuta

Ramatu Garba Baba
November 17, 2021

Kasashen Amirka da Kenya sun nemi a kawo karshen fadan da ake yi a tsakanin rundunar gwamnatin kasar Habasha da 'yan kwatar 'yancin yankin Tigray.

https://p.dw.com/p/437py
Kenia Besuch des US-Außenministers Blinken
Hoto: Simon Maina/AFP/Getty Images

Amirka da Kenya sun kara yin kira na kawo karshen fadan da ake yi a kasar Habasha. Bayan ganawar sakataren harkokin wajen Amirka Anthony Blinken da Shugaba Uhuru Kenyatta na Kenya, sun ce da alamun gwamnatin Habashan za ta iya samar da mafta daga tashin hankali ta hanyar tsagaita bude wuta a fadan da aka kwashi fiye da shekara guda ana yi. Fada ya kazance a tsakanin rundunar sojin gwamnatin Habasha da bangaren da ke yunkurin kwatar 'yancin yankin Tigray, dubbai sun rasa rayukansu wasu sama da miliyan daya na cikin hali na bukatar taimako.

Baya ga haka, Mista Blinken da ke ziyarar aiki a Afrika, inda ya soma da yada zango a kasar Kenya kafin Senegal da Najeriya, ya ja hankalin gwamnatoci da al'ummar nahiyar kan mutunta tsarin mulkin dimukuradiyya da ke fuskantar barazana daga wadanda ke kifar da gwamnati ta hanyar amfani da karfin tuwo.