An zargi kungiyar IS da aikata kisan kare dangi
March 19, 2015Talla
Majalisar Dinkin Duniya ta ce 'yan ta'addar kungiyar IS na aikata kisan kare dangi da kuma ta'asar laifin yaki. Wani rahoto da babbar hukumar kare hakin dan Adam ta Majalisar Dinkin Duniya ta fitar a birnin Geneva ya ce hare-haren da 'yan IS ke kai wa a kan mabiya tsirarun addinai sun yi daidai da kisan kiyashi. Rahoton ya kuma zargi sojojin Iraki da aikata munanan laifuka. Mawallafan rahoton sun yi kira da a mika wannan batu ga kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa da ke birnin The Hague.