1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zargin Sudan ta Kudu da kisan gilla

Yusuf Bala Nayaya
February 13, 2017

Shugaba Salva Kiir na Sudan ta Kudu da wasu manyan jami'ain gwamnatinsa daga kabilar Dinka suna shan zargi bisa kokarin kawar da wata kabila daga doran kasa.

https://p.dw.com/p/2XRnq
Südsudan Präsident Salva Kiir
Hoto: picture-alliance/dpa/P. Dhil

Laftanal Janar Thomas Cirillo Swaka wani babban jami'i a Sudan ta Kudu ya sauka daga kujerarsa sakamakon abin da ya kira sanya hannun gwamnati a yakin basasar kasar, inda ya zargi Shugaba Salva Kiir da wasu manyan jami'an gwamnatinsa daga kabilar Dinka bisa kokari na kawar da wata kabila daga doran kasa.

Ya zargi shugaban da 'yan gani kasheninsa da kokari na mayar da rundunar sojan kasar wani bangare na wata kabila ta kasar ga kisan al'umma a fakaice da aikata fyade da kone kauyuka da yin zagon kasa ga shirin zaman lafiya da 'yan adawa, inda sojan gwamnati ke bin kauyukan 'yan adawa masu son zaman lafiya ta na kisa.

A cewar Swaka da ke zama mai kima a idanun kawayen kasar ta Sudan ta Kudu Shugaba Kiir shi ke jan ragama ta share wata kabila daga kasar da sanya mutane yin kaura ta dole da mamaye wasu al'umma abin da ke zama laifi ne na yaki.