An ɗage tattaunawar sulhun Sudan ta Kudu
February 10, 2014Jami'ai a Addis Ababa na ƙasar Ethiopiya sun ce an ɗage tattaunawar sulhun da aka shirya gudanarwa a wannan litinin tsakanin ɓangarorin dake yaƙi da juna a Kudancin Sudan bayan da aka shafe makonni biyu da ƙulla yarjejeniyar tsagaita wutar da ba ta ɗore ba.
To sai dai tun da fari, Ambassador Mahboub Ma'alim wanda ke zaman babban sakataren ƙungiyar dake raya tattalin arziƙin ƙasashen yankin gabashin Afirka wato IGAD ya faɗawa gidan talibijin na Ethiopiyar cewa a wannan karon tattaunawar za ta mayar da hankali ne kan yin sulhu a siyasance da sasanta tsakanin 'yan ƙasa.
A watan Disemban bara ne yaƙi ya ɓarke tsakanin dakarun dake biyayya ga gwamnati da kuma waɗanda ke biyayya ga tsohon mataimakin shugaban ƙasa Reik Machar, wanda yayi sanadiyyar ƙauracewar dubban 'yan ƙasa, domin tsira da rayuwarsu.
Kawo yanzu dai an dai sakar wa gwamnatin Kenya wasu fursunonin siyasa dake biyayya ga tsohon mataimakin shugaban ƙasar Reik Machar, amma ba a kai ga sannin ko za su kasance a tattaunawar sulhun ba.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Muhammad Nasiru Awal