Ana ci gaba da fafatawa da mayakan IS
December 10, 2014Talla
Wani kiyasi da mahukuntan Kurdana masu kwarya-kwaryar 'yanci daga Iraki, ya nuna yadda aka hallaka mayakan yankin fiye da 700 cikin watanni shida da aka kwashe ana fafatawa da 'yan kungiyar da ke neman kafa daular Islama. Lamarin da ya haifar da 'yan gudun hijira kimanin milyan guda.
Tun watan Yuni mayakan na Kurdawa ke fafatawa da masu neman kafa daular Islama na IS. Lardin na Kurdawa yana da iyaka mai girman kilo-mita 1000 na wuraren da ke zama fagen-daga.
A cikin wata sanarwa rundinar sojin da ake kira Peshmerga ta ce an hallaka mayaka kusan 730, yayin da wasu fiye da 3,500 suka samu raunika, adadin da ya hada da jami'an sojoji, da 'yan sanda gami da masu leken asiri.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Piando Abdu