1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da gumurzu a Sudan ta Kudu

Mouhamadou AWal BalarabeMarch 17, 2015

'Yan tawayen Sudan ta Kudu sun yi amai sun lashe inda suka tabbatar da fada tsakaninsu da dakarun gwamnati bayan da suka fara karyata wannan labari

https://p.dw.com/p/1Es7d
Hoto: Reuters

'Yan tawayen Sudan ta Kudu sun tabbatar da cewa suna mummunan gurmuzu tsakaninsu da dakarun gwamnati a yankin Nilu da ke da arzikin man fetur. Wannan ya zo ne kwana daya bayan da gwmantin Salva Kiir ta bayyana cewa ta kashe 'yan tawaye da dama a kusa da Renk, lamarin da 'yan tawaye suka musanta.

Bangarorin biyu na ci gaba da zargin junansu da fara kai hari a wannan yanki da kusa da kasar Sudan. Da ma dai shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir da kuma tsohon mataimakinsa Riek Machar sun saba keta yarjejeniyoyin zaman lafiya da suka cimma.

Tun dai a karshen shekara ta 2013 Sudan ta Kudu ta sake fadawa cikin tashin hankali da zubar da jini sakamakon neman kakkage madafun iko da bangarorin biyu ke yi. Babu dai wanda ya san adadin mutanen da suka rigamu gidan gaskiya tun bayan barkewar rikicin, amma kuma majalisar Dinkin Duniya ta nunar da cewa 'yan Sudan ta Kudu miliyan biyu ne suka kaurace wa matsugunsu.