1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ana ci gaba da gwabza fada a Sudan

Binta Aliyu Zurmi
May 25, 2023

Bangarorin da ke gaba da juna a kasar Sudan na nuna yatsa ga junansu a kan gaza mutunta yarjejeniyar tsagaita wuta ta mako guda da aka cimma da taimakon kasashen Amirka da Saudiyya.

https://p.dw.com/p/4RpSH
Sudan Khartoum | Waffenruhe
Hoto: AFP/Getty Images

Yarjejeniyar da a yau ta shiga rana ta uku ana ci gaba da jiwo amon harbe-harbe a sararin samaniyar kasar.

Da ma dai an cimma tsagaita wutar ne domin bada kofar kai agajin gagawa ga mabukata da har yanzu ke makale a cikin kasar.

Wannan shi ne karo na 4 da ake cimma yarjejeniyar tsagaita wuta wanda kamar sauran ta baya ba a mutunta ta ba.

Tun a tsakiyar watan Afirilu rikicin shugabanci ya barke a tsakanin sojojin gwamnati karkashin Janar Abdel fatah al-Burhan da na dakarun sa kai na RSF da Mohammaed Hamdan Daglo ke jagoranta.

Janar Abdel Fattah al-Burhan ya sanar da tsige madugun 'yan tawayen na RSF Mohamed Hamdan Dagalo a matsayin mataimakinsa.