1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana ci gaba da gwabza fada a Sudan

June 11, 2023

Bayan mutumta yarjejeniyar tsagaita buda wuta ta sa'o'i 24 bangarorin da ke fada a Sudan sun ci gaba da gwabza fada a wannan Lahadi.

https://p.dw.com/p/4SRwk
Wasu gine-gine a birnin Khartun na Sudan
Wasu gine-gine a birnin Khartun na SudanHoto: - /AFP/Getty Images

Rahotanni daga Sudan na cewa an wayi garin yau a birnin Khartum cikin amon manyan bindigogi jim kadan bayan cikar wa'adin yarjejeniyar tsagaita buda wuta ta sa'o'i 24 wace ta ba wa mazauna birnin damar numfasawa bayan kwashe kusan watanni biyu cikin kazamin tashin hankali.

Kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP ya ruwaito mazaunan wasu anguwannin birnin na cewa tun da sanyin safiyar nan suka fara jin karar manyan makamai tare da hango gajimaren hayaki ya turnike a kusa da matatar mai ta Al-Shajara da ke Khartum.

An kuma ci gaba da gwabza fadan a yankin Darfur inda kungiyoyin agaji na kasa da kasa suka bayyana damuwa a game da rincabewar al'amura.

A wannan Jumma'a da ta gabata ma dai shugaban tawagar jami'an agaji na Red Cross da ke kasar Alfonso Verdu Perez ya yi gargadin cewa kashi 20% kadai ne da ma'aikatun kiwo lafiya ke aiki a birnin na Khartum inda a nan ne fadan ya fi kamari.