1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana cigaba da samun karin haske kan maharan Paris

Ahmed SalisuNovember 14, 2015

Hukumomi a Paris sun ce suna samun karin haske game da wanda suka kai harin birnin Paris na ranar Juma'a inda mutane 128 suka rasu kana wasu 350 suka jikkata.

https://p.dw.com/p/1H5cq
Frankreich Paris Terroranschläge Trauer
Hoto: DW/L. Scholtyssyk

Ya zuwa yanzu dai an bayyana suna guda daga cikin maharan wanda aka gano. Sunan mutumin dai Omar Isma'il Mostefai dan shekaru 29 da haihuwa wanda aka haifa a kasar ta Faransa. Mostefai dai inji jami'an tsaron sanannen bata gari ne kuma mutum ne mai son batun da ya danganci tsaurin kishi na addini. A wani labarin kuma, Girka ta ce daya daga cikin maharan ya shiga Turai ta kasarta ne kafin ya isa Paris don gudanar hare-haren da aka kai.

A kasar Belgium kuwa hukumomi sun ce bincike da suka yi bayan da suka yi kame jiya a birnin Brussel ya nuna musu cewar wanda suke tsare da su na da alaka da wanda suka kai hare-haren birnin na Paris. Magajin garin Molenbeek da ke Brussels Francoise Schepmans ne ya bayyana hakan dazu sai dai bai yi karin haske ba.

Kungiyar IS dai ta ce ita ce ta kai harin na Paris. A wani sako da ta fidda, ta ce mayakanta za su cigaba da haka muddin Faransa ba ta sauya tsarinta na yakarsu ba. Yanzu haka dai birnin na cike da jami'an tsaro inda rahotanni ke cewar yawan jami'an ya kai dubu da dari biyar. Shaguna da sauran wuraren haduwar jama'a na cigaba da kasancewa a rufe a rana ta biyu ta zaman makoki da ake yi.

Kasashen duniya na cigaba da aikewa da sakonninsu na alhini da ta'aziyya ga al'ummar Faransa bayan jerin hare-haren. Shugaba Barack Obama na Amirka ya ce harin na Paris hari ne kan al'ummar duniya baki daya inda ya kara da cewar ''za mu yi aiki da mahukuntan Faransa da sauran kasashen duniya wajen ganin an hukunta wanda ke da hannu a wannan mummunan aiki kana za mu tinkari 'yan ta'adda a ko ina suke don kawar da su.''

Frankreich Terroranschläge Militär
Hoto: Reuters/Y. Herman

Jamus ma dai tayin tallafi ta yi ga Farasan da nufin ganin na kame wanda ke da hannu a harin da aka kai kana ta ce harin. Turkiyya ma dai ta bi sahun kasahen duniya wajen nuna alhinita inda firaministan kasar Ahmet Davutoglu ya ce harin wani yunkuri ne na yin karen tsaye ga tsarin dimokradiyya da 'yancin walwala. Shugaban Iran Hassan Rouhani a nasa martanin ya ce harin wani aiki ne ta'addanci kuma kasashen duniya za su gama kai wajen ganin bayan masu irin wannan dabi'a.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani

Nuna karin labarai