1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana fafatawa tsakanin dakarun ƙawance da ´yan tawayen Taliban

May 26, 2007
https://p.dw.com/p/BuKm
An kashe wani sojin kungiyar tsaro ta NATO tare da jiwa hudu rauni a wani hari da aka kai kansu a kudancin Afghanistan da sanyin safiyar yau asabar. Hakan ya auku ne a daidai lokacin da sojojin kawance karkashin jagorancin Amirka hade da dakarun Afghanistan suka tsare wani kwamandan kungiyar Taliban da kuma wasu mutane biyu da ake zargi ´yan tawayen kungiyar al-Qaida ne. Jami´ai sun nunar da cewa sojin na kungiyar NATO ya gamu da ajalinsa yayin wani farmaki da sojojin kawance ke kaiwa ´yan Taliban. Ba´a dai bayyana kasar da sojin ya fito ba da kuma wurin da aka fafatar ba. A jiya juma´a wani bam da aka dana a gefen hanya ya halaka sojin Kanada a lardin Kandahar.