Ana farautar wanda suka kai harin Pakistan
March 28, 2016Talla
A wani sako da ya sanya shafin Twitter, mai magana da yawun rundunar sojin kasar ta Pakistan Asim Bajwa ya ce an kame 'yan ta'adda dama wanda ake zargin suna da hannu a harin na ranar Lahadi sai dai ba yi karin haske ba game da yawansu ko wuraren da aka yi kamen ba.
Kimanin mutane 72 wanda galibinsu yara ne suka rasu a wani wajen wasa yayin da wasu karin mutanen da yawansu ya kai dari hudu suka jikkata, wasunsu ma munana.