Ana fargabar aukuwar bala'in aman wuta
November 27, 2017Talla
An dauki matakin kwashe dubban mutane daga wasu wuraren da ke kan hadarin fuskantar bala'in a wannan Litinin. Wuraren da matsalar ta shafa sun hada har da babban filin jirgin yankin da ke da dubban matafiya.Alamun aman na wuta sun bayyana ne a makon da ya gabata, lokacin da aka ga wani hayakin da ke nuna yi yuwar bala'in ya tirnike wani tsauni mai nisan sama da kilomita 3 zuwa sararin samaniya.
Fargabar ta tilastawa hukumomi dakatar da zirga-zirgar jirage a yankin tsibirin na Bali. Mutane sama da dubu 40 da ake ganin lamarin zai iya shafa sun kauracewa yankin, yayin da a bangare guda hukumomin kasar ta Indonesiya suka yi shelar kwashe wasu karin mutum dubu 100 da ka iya shiga cikin wannan hatsari.