Joe Biden na halartar taron kungiyar Nato
June 14, 2021Ana gudanar da babban taron shugbbanin kungiyar tsaro ta NATO a birnin Brussels na kasar Beljiyam inda a karon farko shugaban Amirka Joe Biden ke halarta tun bayan maida kasarsa a cikin kungiyar da tsohon shugaba Donald Trump ya fidda.Shugaba Biden zai tattauna da sauran shugabbanin kungiyar a kan bukatar daukar matakan hadin kai domin dakatar da barazanar da kasashen China da Rasha ke yi.Rahotanni sun ce shugaban na Amirka zai jaddada matsayarsa na mutunta ayar dokar kungiyar da ta ce hari a kan kasa daya da ke kungiyar tamkar hari ne a kan duk kasashe mambobinta.
Daga cikin mahalarta taron har'da shugaban Kasar Turkiyya Racep Tayyip Erdogan wanda ya ce yana fatan haduwarsa da Joe Biden za ta kawo karshen tsamin dangantakar da ke tsakanin kasashensu.