Ana jajibirin zaben shugaban kasa a Brazil
October 29, 2022Talla
'Yan takarar shugaban kasar Brazil na can suna karkare gangaminsu na yakin neman kuri'u, yayin da ranar Lahadi za a yi zabe zagaye na biyu a kasar.
Tsohon shugaban kasar Luiz Inacio Lula da Silva, wanda wasu ke zargi da almundahana, shi ne ke da alamun samun rinjaye bayan sha da kyar da ya yi a zagayen farko na zaben da aka yi a ranar biyu ga wannan wata na Oktoba.
Kasar ta Brazil dai na fama da matsalolin tattalin arziki da dama, abin da ake ganin kasar na bukatar wanda zai fidda ta ita daga kangin da take ciki.
Takara ce dai a tsakanin Shugaba Jair Bolsonaro mai ci a halin yanzu da kuma tsohon shugaban kasar, Luiz Inacio Lula da Silva.