1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana jirar sakamakon zaben shugaban kasar Senegal

February 25, 2007
https://p.dw.com/p/BuR9

An kammala kada kuri´a a zaben shugaban kasar Senegal da aka gudanar yau. Shugaba Abdulaye Wade mai shekaru 80 na fatan sake lashe zaben don yin sabon wa´adi na shekaru 5 akan mulki. To sai dai yana fuskantar kalubale daga sauran ´yan takara 14 a wannan kasa dake da zaunanniyar demukiradiya a jerin kasashen Afirka. Shugaba Wade wanda ya fara lashe zabe a watan maris na shekara ta 2000 ya na da karfin guiwar samun kashi 50 cikin 100 na kuri´un da aka kada, don kauracewa zuwa zagaye na biyu. A martanin da ya mayar ga masu kira garweshi da ya yi ritaya, shugaba Wade cewa yayi:

“Ya rage ga al´umar Senegal sun yanke hukunci. Idan a garesu na tsufa ba zan iya tabuka komai ba, to ba zasu jefa mini kuri´un su ba."

Rahotanni sun nunar da cewa masu zabe musamman a birnin Dakar sun fita kwansu da kwarkwatansu don kada kuri´a. Sama da mutane miliyan biyar suka cancanci kada kuri´a a kasar mai yawan al´uma miliyan 11 da dubu 700.