1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana kappa-kappa a biranen Kenya

October 28, 2017

Manyan garuruwan kasar sun kasance tsit a ranar Asabar, bayan hatsaniyar siyasa da kasar ta sami kanta ciki, inda ya kai ga asarar rayuka sakamakon arangama tsakanin jami'an 'yan sanda da kuma 'yan adawa.

https://p.dw.com/p/2mfW6
Kenia Wahlen
Hoto: picture-alliance/AP Images/S.Abdul Azim

Rahotanni daga kasar Kenya, na cewa manyan garuruwan kasar sun kasance tsit a wannan Asabar, bayan hatsaniyar siyasa da kasar ta sami kanta ciki, inda ya kai ga asarar rayuka sakamakon arangama tsakanin jami'an 'yan sanda da kuma 'yan adawa. Shaidu sun ce a birnin Kisumu, birni da ke dauke da galibi 'yan bangaren adawa, da ma wasu sassa na Nairobi babban birnin kasar sun kasance cikin dari-darin gudanar da harkoki.

Hukumar zaben kasar dai ta jinkirta zabe a gundumomi hudu daga cikin 47 da ake da su a kasar ne saboda tashin tarzomar da ta ce hatsari ga jami'an zabe musamman. Magoya bayan madugun adawar kasar Raila Odinga, sun sha alwashin ci gaba da bijirewa duk wani shiri da za a yi don sake zabe a yankunan da su din, suka hana yiwuwarsa.