1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana samun galaba kan mayakan IS a Iraki

Ahmed SalisuMay 23, 2015

Rundunar sojin Iraki ta ce ta karbe iko da wani yanki da ke gabashin Ramadi wanda 'yan kungiyar nan ta IS suka karbe iko da shi a yunkurinsu na girka daular Islama.

https://p.dw.com/p/1FVQS
Irak Milizen
Sojin Iraki sun samu wannan nasara ce da taimakon soji sa kai na Sunni da na 'yan Shi'aHoto: Getty Images/AFP/A. Al-Rubaye

Wani jami'in tsaro da ya zanta da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP bisa sharadin za a sakaye sunansa ya ce yanzu haka dakarun gwamnati ne ke iko da yankin Husaybah kuma sun danna kai don kubutar da lardin Jweibah.

Wannan nasara da sojin Iraki suka samu tare da tallafin sojin sa kai da ke bin tafarkin Sunni da Shi'a a yankin na zuwa ne daidai lokacin da dakarun kawancen da Amirka ke jagoranta a yaki da 'yan IS ke kara matsa kaimi wajen kai hari kan mayakan IS din a Ramadi tun daga jiya Juma'a.