Ana samun galaba kan 'yan Jihadin Iraki
August 21, 2014Dakarun Kurdawan sun kame galibin yankin babbar madatsar ruwan ta Mosul sakamakon yadda Amirka da Birtaniya suka kara kaimin kai hare-hare ta sama kan mayakan kungiyar da ke neman kafa wata daular Islama. Wannan lamari ya zama gagarumin koma baya ga mayakan masu kaifin kishin addinin Islama, duk da yake ba su mika wuya cikin sauki ba.
An ji karar fashe-fashe lokacin da ake fafatawa tsakanin bangarorin. Wani kakakin sojin Iraki ya tabbatar da cewa madatsar ruwan ta koma karkashin ikon gwamnati. A farkon wannan wata na Agusta mayakan dauke da makamai suka kwace iko da madatsar ruwan, wadda take taimakawa wajen samar da wutar lantarki ga miliyoyin mutane. Madatsar ruwan da dakarun gwamnatin suka kwato daga mayakan na zama daya daga cikin abubuwa da tsohon Shugaban Iraki Marigayi Saddam Hussein ya aiwatar a shekarun 1980 da taimakon injiniyoyin kasar Jamus ta Gabas a lokaci, da har yanzu al'ummar kasar ke ci gaba da samun moriya.
Karin taimako daga kasashen yamma
Frank-Walter Steinmeier ministan harkokin wajen Jamus da ya kai ziyara Bagadaza babban birnin kasar ta Iraki ya nunar da shirin kasashen yammaci na kara taimaka wa kasar:
"Bugu da kari abin da muka tattaunawa da sauran kasashen mambobin kungiyar Tarayyar Turai shi ne hanyoyin da za a taimaka wa wadanda suke yakar 'yan kungiyar ta IS."
Tuni taimako na farko da Jamus ta tura na kayayyakin tallafi suka isa birnin Erbil na yankin Kurdawa. Taimakon ya haura na dala milyan 24 kamar yadda ministan harkokin wajen kasar ta Jamus, Frank-Walter Steinmeier ya bayyana.
Halin kunci ga 'yan gudun hijira
Mayakan da ke neman kafa daular Islama sun yi kaurin suna inda suka bayar da kimanin mutane dubu 400 'yan gudun hijira a yankin Kurdawa na kasar ta Iraki. Sannan suna gallazawa ko kashe duk wanda ya ki amincewa da ra'ayi irin nasu. Ga daya daga cikin wadanda suka tsira daga hare-haren tsagerun.
"Ba mu da komai. Muna mutuwa sakamakon yunwa da kishin ruwa. Mun kwashe kwanaki 12 muna tafiya, wasu sun mutu wasu kuma sun galabaita."
Ita ma wannan mata da ta tsira ta ba da mummunan labarin abin da ya faru da sauran mutanen da suka tsere tare.
"Na yi sa'a iyalaina sun tsira amma wasu abokaina sun mutu. Akwai iyalan da aka kashe baki daya."
Fatan da ake da shi na iya sake dinke rikicin da kasar ta Iraki ke fuskanta shi ne yadda duk bangarorin kasar suka shiga tattaunawa ta kafa sabuwar gwamnati da Haider al-Abida yake yi, bayan da Firaministan mai barin gado Nouri al-Maliki ya rungumi kaddara.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mohammad Nasiru Awal