Ana shiga yajin aiki a Sudan
May 28, 2019Talla
Hakan dai wani kokari ne na ci gaba da matsa wa sojojin kasar lamba don ganin sun mika mulki ga gwamnatin farar hula.
Sojojin kasar da suka karbe mulki daga hannun tsohon Shugaba Omar al Bashir cikin watan jiya, sun gaza cimma matsaya da jagororin kungiyoyin fararen hula kan yadda za a sama wa kasar alkibla.
Jagororin zanga-zangar sun ce yajin aikin zai hada da likitoci da alkalai da lauyoyi da ma'aikatan ruwa da wuta.
Haka ma abin yake ga bangaren sufurin jiragen sama da na kasa da ma bangaren sadarwa.
Kafin wannan matakin dai, an ga shugabannin gwamnatin kasar na ziyarce-ziyarcen kulla alaka da wasu kasashen larabawa.