ANA TA KARA SAMUN RASHIN JITUWA TSAKANIN MINISTAN TATTALIN ARZIKI DA MINISTAN KARE MUHALLI NA TARAYYAR JAMUS
March 23, 2004Babu abin da yi fi muhimmanci ga ministan tattalin arzikin tarayya, Wolfgang Clement, kamar ganin cewa, an sami sassaucin cijewar al’amura, wadda a halin yanzu ke addabar harkokin tattalin arzikin Jamus. Sabili da haka ne kuwa, yake daddage wa duk wani matakin da yake zaton zai kasance wani shinge ne ga masana’antu, wajen tafiyad da harkokinsu. Wannan matsayin da ministan ya dauka dai, ya janyo wata hauhawar tsamari tsakanin ma’aikatarsa da ma’aikatar kare muhalli ta tarayya, wadda ke fafutukar ganin cewa, gwamnati ta dau tsauraran matakai don tilasa wa masana’antun nan kasar, aiwatad da ka’idojin yarjejeniyar nan ta Kyoto. Ita dai wannan yarjejeniyar ta tanadi rage yawan hayakin da masana’antu ke fitarwa ne, mai janyo dumamar yanayi. A ganin ministan tattalin arziki Clement dai, Jamus na kan gaba wajen daukan matakan kare muhalli. Sabili da haka ne ya ga bai kamata a matsa wa masana’antun kasar nan lamba ba, wajen daukan wasu matakan kuma. A cikin wata fira da ya yi da gidaj talabijin nan na ARD, ministan ya bayyana cewa:-
"Mu ne kan gaba a duniya. Amma idan muka ci gaba da daukan matakan, za mu saura ne mu kadai can gaba. Hakan kuwa ba zai yiwu ba. Kamata ya yi, farkon kasashe uku a jerin kasashen masu ci gaban masana’antu, su bi misalan mu wajen daukan matakan kare muhallin. Idan ko ba haka ba, mu ne za mu yi asara a fagen tsererniyar kasuwancin duniya. Wannan dai ita ce babbar matsalar."
Ban da yunkurin kare masana‘antun Jamus da yake yi, ministan tattalin arzikin ya kuma sanya tambayar alama a kan harajin da gwamnati ta sanya kan kafofi da masana’antun da ke janyo gurbacewar yanayi, wajen sarafa kayayyakinsu. Yin hakan dai ya fusatad da `yan jam’iyyar Greens, abokiyar kawancen jam’iyyar SPD a gwamnatin hadin gwiwa ta tarayya. Furucin da ministan ya yi, ya sa ana ta yada rade-radin cewa, gwamnati za ta soke wannan harajin. Kai tsaye ne dai, kakakin gwamnatin tarayya, ya kira taron maneman labarai, inda ya musanta wannan zaton da ake yi.
A nasa bangaren, ministan kare muhalli, Jürgen Trittin, ya yi kokarin dusashe kaifin tsamarin da ake samu tsakaninsa da ministan tattalin arzikin ne da cewa:-
"Ina fahimtar kalubalen da ministan tatalin arzikin ke huskanta, a yunkurin da yake yi na cim ma wata madafar da masana’antu da kuma bangaren kare muhalli za su amince da ita. Muna tuntubar juna, kamar dai yadda muka saba. A tattaunawar da ake yi kan wannan batun dai, ba za a cim a wani sakamako ba, sai an takalo duk al’amuran da suka shafi tsarin aiwatad da shirin. A halin yanzu dai a mu kai ga nan ba tukuna. Sabili da haka, yada rade-radi, ba ta da wata ma’ana."
Wakilan kungiyoyin masana’antu dai na zargin ministan kare muhallin ne, da tilasa wa kamfanonin Jamus bude rassa a kasashen ketare, saboda tsauraran ka’idojin kare muhallin da ya shimfida musu a nan cikin gida. Hakan kuma ne ke janyo karin yawan marasa aikin yi da ake ta samu a nan kasar. Su ko kungiyoyin kare muhalli, gani suke yi, ministan tattalin arzikin ne ummal aba’isin rikicin da ya barke a halin yanzu, saboda nuna rashin fahimta ga muhimmancin da matakan kare muhalli ke da shi.
A bayan shinge dai, wasu majiyoyi masu tushe na nuna cewa, akwai `yan majalisar ministoci da dama da ke kira ga shugaba Schröder, da ya tsoma baki a wannan jayayyar da ministocin biyu ke yi, don ya ga cewa, an fara aiwatad da ka’idojin kare muhallin, kamar yadda minista Trittin ya bukaci a yi.
A cikin `yan watanni kadan masu zuwa ne, shugaban zai bude wani taron kasa da kasa a birnin Bonn, don tattauna batun samar wa duniya makamashi maras gurbata yanayi. Ana zaton cewa, fiye da kasashe 80 ne za su halarci taron. To ashe kuwa, kamata ya yi gwamnatin tarayyar ta nuna misali a zahiri a fannin kare muhalli, don ta iya shawo kan sauran kasashe su fahimci cewa, fafutukar da ake yi ta kawo karshen gurbata yanayi, guri ne mai ma’ana, wanda kuma ba za a iya cim masa ba sai da hadin kai.