1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana tattauna makomar shugabar kasar Brazil

Salissou BoukariApril 15, 2016

Majalisar dokokin Brazil ta soma muhawara a wannan Jumma'a kan matakin tsige shugaban kasar Dilma Rousseff bisa zargin rufa-rufa kann tattalin arzikin kasa.

https://p.dw.com/p/1IWad
Brasilien Bundesverfassungsgericht
Hoto: Agência Brasil/Antonio Cruz

Shugabar kasar ta Brazil Dilma Rousseff ta shigar da wannan batu ne a gaban babbar kotun kolin kasar, inda alkalan kotun suka shafe awowi takwas da yammacin ranar Alhamis suna tattauna lamarin, kafin da tsakiyar dare mafi yawan alkalan suyi watsi da wannan kara da shugabar kasar ta shigar a gabansu na neman a yi watsi da wannan mataki.

Tsawon kwanaki uku ne dai 'yan Majalisar za su dukufa kan laifukan da ake zargin shugabar kasar da aikatawa, kafin daga bisani su yanke hukunci kan makomarta a ranar Lahadi inda za su kada kuri'ar yakar kauna.

Idan suka yi nasarar tsigeta, za a maye gurbinta da mataimakin shugaban kasar ta Brazil