1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ana zabe a wasu kasashe shidda na nahiyar Afirka

Ahmed SalisuMarch 20, 2016

Jama'a a wasu kasashe shidda na Afirka na cigaba da kada kuri'unsu a zabukan da ke wakana a kasashensu ciki har da Jamhuriyar Nijar.

https://p.dw.com/p/1IGfJ
Sudan Wahlen
Hoto: AFP/Getty Images/P. Baz

A Jamhuriyar Nijar inda ake zagaye na biyu na zaben shugaban kasa ana takara ne tsakanin shugaba mai ci Issoufou Mouhamadou na jam'iyyar PNDS da kuma Hama Amadou na Moden Lumana Afirka da ke adawa sai da jam'iyyar ta Lumana da sauran jam'iyyun adawa sun kauracewa zaben bisa ga abinda suka rashin adalci da kura-kuran da aka yi a zagayen farko na zaben da ya wakana.

Can ma kasar Benin yau ne ake zagaye na biyu na zaben shugaban kasa inda firaministan kasar Lionel Zinsou da attajirin nan Patrice Talon ke zawarcin kujerar shugaban kasa. 'yan adawa a kasar dai sun hadu sun marawa Mr. Talon baya a zaben. An samu fitar jama'a sosai a zaben sabanin yadda aka gani a Jamhuriyar Nijar inda 'yan adawa suka kauracewa zaben.

Niger Hamdoullaye Wählerinnen
Hoto: DW/M. Kanta

A yankin Zanzibar na kasar Tanzaniya ma zabuka na gudana sai dai ba a sami fitar mutane ba amma kuma komai na wakana lafiya kamar yadda babban baturen 'yan sanda a yankin ya shaida Mkadam Khamis ya shaidawa DW. A share guda kuma wani jigo na 'yan adawa a yankin ya ce sun yaba da yadda jama'a suka ki fitowa zaben inda ya kara da cewar ba za su amince da duk wani sakamako da zai fito daga zaben ba.

Al'ummar kasar Kongo da Cape Verde ma dai kamar takwarorinsu na zabe na shugaban kasa. Can din ma dai babu wani ahoto da muka samu na tashin hankali. A Senegal kuwa zabe ake yi na raba gardama kan gyara ga kundin tsarin mulki kasar. Shugaban kasar Macky Sall ya kira zaben ne don jama'a sun bayyana ra'ayinsu game da rage yawan shekraun da shugaba zai yi kan mulki daga 7 zuwa 5. Wannan ne karon farko da wani shugaba a Afirka ya taba yin haka.